Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 15:24:58    
Kyakkyawan birni na Chongqing

cri

'Na shiga jirgin ruwa a tashar jiragen ruwa na Chaotianmen da ke Chongqing. Na ji farin ciki sosai a lokacin da jirgin ruwan na tafiya sannu sannu a kan kogin. Na iya zaunawa a kan jirgin ruwan ko kuma barandar dakin da ke cikinsa domin ganin manyan tsaunuka da kwazazzabai da kauyuka. Ina tafiya cikin ni'imtattun wurare kamar yadda nake cikin wani fim.'

Saboda ana gudanar da babban aikin yin amfani da ruwa na Sanxia, ana tattara ruwa, shi ya sa Sanxia ta fito da wasu sabbin wuraren yawon shakatawa.

Mutum-mutumin sassaka na Dazu wurin yawon shakatawa ne da ya fi kyau a kai mata ziyiara. Tarihinsa ya wuce shekaru dubu daya. Mutum-mutumin sassaka na addinin Buddha sun sami rinjaye a nan tare da wasu na addinin Tao da na Confucius. Kungiyar UNESCO ta tanadi mutum-mutumin sassaka na Dazu a cikin takardar sunayen kayayyakin tarihi na al'adu na duniya a shekarar 1999.

Bayan da madam Hilde Andresen, wadda ta zo daga birnin Frankfurt na kasar Jamus ta ji dadin ganin wasu mutum-mutumin da aka sassaka na Dazu, ta bayyana cewa,

'Mutum-mutumin sassaka da na gani sun burge ni sosai. Ban taba samun damar ganin irin wadannan abubuwan fasaha da kuma sanin tahirinsu a da ba.'

Dadin dadawa, birnin Chongqing ita kanta wurin yawon shakatawa ne da ya yi suna a kasar Sin. Kogin Yangtze da kogin Jialingjiang suna garkuwa da tsakiyar birnin, gine-gine iri daban daban suna dab da tsaunuka da kuma koguna. Wannan birni ya fi kyau gani a dare.


1 2 3