Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 11:06:07    
Kungiyar 'yan kwadago ta kasar Sin tana binciken matsalar yin amfani da 'yan kwadago ba bisa doka ba

cri

Yanzu, babbar kungiyar 'yan kwadago ta kasar Sin da ma'aikatar kula da harkokin 'yan kwadago da ma'aikatar tsaron zaman lafiyar jama'a ta kasar Sin suna ci gaba da binciken matsalar da ta auku a haramtattun masana'antun yin bulo a lardin Shanxi. Babbar kungiyar 'yan kwadago za ta mai da hankali kan yadda ake binciken wannan matsala, kuma za ta nemi kungiyoyin 'yan kwadago na wurin da su halarci wannan aiki domin tabbatar da ikon halal na 'yan kwadago wadanda suka sha wahala a cikin matsalar. A waje daya kuma, babbar kungiyar 'yan kwadago ta kasar Sin za ta mai da hankali da sa kaimi kan masana'antu wajen binciken matsalolin yin amfani da 'yan kwadago ba bisa doka ba domin kara tabbatar da ikon halal na 'yan kwadago da na 'yan cirani. Mr. Zhang ya ce, "Sannan kuma, ba ma kawai babbar kungiyar 'yan kwadago ta kasar Sin da kungiyoyin 'yan kwadago na matakai daban-daban na lardin Shanxi za su shiga aikin binciken wannan matsalar yin amfani da 'yan kwadago ba bisa doka ba, har ma za mu kara mai da hankali kan yadda ake kafa kungiyoyin 'yan kwadago a dukkan masana'antu domin kara yawan kungiyoyin 'yan kwadago a cikin masana'antu. Bugu da kari kuma, za mu gabatar da ra'ayoyinmu ga hukumomin gwamnatin da abin ya shafa wajen tabbatar da ikon halal na 'yan kwadago, musamman na 'yan cirani."(Sanusi Chen)


1 2 3