
Kwanan nan, matsalar yin amfani da 'yan kwadago yara da wulakanta 'yan kwadago a cikin wasu haramtattun masana'antun yin bulo na lardin Shanxi tana jawo hankulan duk zaman al'ummar kasar Sin. Babbar kungiyar 'yan kwadago ta kasar Sin tana kuma shiga aikin ceton 'yan kwadago da binciken masu mallakar irin wadannan haramtattun masana'antu. Ya zuwa yanzu, an riga an ceci 'yan kwadago da yawa.
A ran 18 ga wata, babbar kungiyar 'yan kwadago ta kasar Sin ta shirya wani taron manema labaru a nan birnin Beijing, inda aka sanar da labari kan yadda ake binciken irin wadannan matsaloli. Mr. Zhang Mingqi wanda ke yin wannan bincike ya ce, "Bisa binciken da muka yi, ya zuwa yanzu an riga an cafke Wang Bingbing wanda ke mallakar wannan haramtacciyar masana'antar yin bulo a lardin Shanxi. A waje daya, bisa dokokin kasar, an kuma haramta wa wannan masana'anta yin amfani da dukkan kudadenta. Bugu da kari kuma, a ran 16 ga wata a lardin Hubei, an riga an cafke Heng Tinghan, wani mutum wanda ke kula da harkokin yau da kullum na wannan masana'antar yin bulo. Sabo da haka, an riga an cafke dukkan mutanen da ake tuhumarsu cewa suna da hannu a cikin wannan matsala."
1 2 3
|