Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 11:06:07    
Kungiyar 'yan kwadago ta kasar Sin tana binciken matsalar yin amfani da 'yan kwadago ba bisa doka ba

cri

Wannan matsalar yin amfani da 'yan kwadago yara da wulakanta su ta auku ne a wata masana'antar yin bulo da ke kauyen Caosheng na gundumar Hongdong ta lardin Shanxi. Wadanda suke mallakar wannan masana'anta sun dade suna wulakanta 'yan kwadago. Bisa binciken da aka yi, an ce, wannan matsala tana daya daga cikin irin wadannan matsalolin da ke kasancewa a lardin Shanxi. An bayyana cewa, ya zuwa ran 17 ga watan Yuni, an riga an ceci 'yan kwadago fiye da 370 daga cikin irin wadannan haramtattun masana'antun yin bulo na lardin Shanxi.

Mr. Zhang Mingqi ya bayyana cewa, kiyaye ikon halal na 'yan kwadago yana daya daga cikin muhimman nauyin da ke bisa wuyan kungiyoyin 'yan kwadago na matakai daban-daban, dole ne su kansace kan gaba wajen tabbatar da ikon halal na 'yan kwadago. A waje daya, ya kamata su yi bincike daga duk fannoni kan yadda ake amfani da 'yan kwadago ba bisa doka ba domin yin yaki da haramtattun ayyuka na yin amfani da 'yan kwadago da 'yan kwadago yara ba bisa doka ba da haramtattun ayyuka na wulakanta da keta hakkin 'yan kwadago da ikonsu na halal. Dole ne kungiyoyin 'yan kwadago wadanda suke matsayin tabbatar da ikon halal na 'yan kwadago a madadinsu su halarci ayyukan tabbatar da ikon halal na 'yan kwadago da wasu hukumomin shari'a suke aiwatarwa.


1 2 3