Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-18 11:15:30    
Ja-in-ja da Mahmoud Abbas da kungiyar Hamas ke yi a tsakaninsu na kara tabarbarewa

cri

Yanzu, kungiyar Hamas ta ce, gwamnatin gaggawa ba ta dace da doka ba, ta ki amincewa da ita, kuma ba za ta ba da hadin kai gare ta ba. Sa'an nan kuma Sami Abu Zuhri, kakakin kungiyar Hamas ya ce, kungiyar ta shiga cikin zukatun Falasdinawa sosai, don haka za ta ci gaba da yin dagiya.

Manazarta sun nuna cewa, yayin da manyan rukunoni biyu na Falasdinu ke ja-in-ja a tsakaninsu a fannin siyasa a yanzu, kungiyar Fatah wadda ke karkashin shugabancin Abbas tana tsayawa a kan matsayi mai rinjaye kadan, musamman ma ta sami goyon baya sosai daga wajen gamayyar kasa da kasa sabo da mataki da ta daukai wajen kafa gwamnatin gaggawa. Amma game da batun ikon mallakar rundunar sojoji, sojojin kungiyar Hamas sun riga sun tsaya kan matsayin soja mai rinjaye a Zirin Gaza bayan da ta yi yaki a jere. Sabo da haka, ja-in-ja da bangarorin biyu ke yi a tsakaninsu zai kara tabarbarewar wannan batu.(Halilu)


1 2 3