Kazalika shelar da Abbas ya yi cewa an haramta bangaren soja na kungiyar Hamas, wannan ma wani tsattsauran mataki ne da ya dauka don murkushe kungiyar. A cikin umurnin shugaba da ya sa hannu a kai, an nuna cewa, da ganin yadda rundunar sojojin zartaswa da bangaren soja Izz A Din Al_Qassam Brigades na kungiyar Hamas suka yi juyin mulkin soja a zirin Gaza, sun saba wa doka da tsarin mulki na Falasdinu, don haka ya yanke shawarar haramta su. Haka kuma zai yanke hukunci a kan mutane da abin ya shafa bisa dokar ta baci da sauran dokoki. Manazarta suna ganin cewa, a hakika dai, Abbas ya yi amfani da wannan dama don yin tir da juyin mulkin soja da bangaren soja na Hamas ya yi, don neman daidaita batun artabu da ake yi tsakanin rukunoni biyu sabo da ikon mallakar rundunar soja ta Falasdinu.
Wata majiyar Ramallah ta bayyana cewa, bayan kafuwar gwamnatin gaggawa, Abbas zai ki tattaunawar da zai yi da kungiyar Hamas. Sa'an nan yana kokari sosai wajen neman gamayyar kasa da kasa da ta nuna goyon baya ga gwamnatin gaggawa.
1 2 3
|