Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-18 11:15:30    
Ja-in-ja da Mahmoud Abbas da kungiyar Hamas ke yi a tsakaninsu na kara tabarbarewa

cri

Ran 17 ga wata da tsakar rana, Mahmoud Abbas, shugaban Falasdinu ya rantsar da gwamnatin gaggawa a birnin Ramallah da ke gabar yammacin Kogin Jordan, don maye gurbin gwamnatin hadin kan al'ummar Falasdinu wadda Abbas ya yi watsi da ita a ran 14 ga wata da dare. A wannan rana, Abbas ya bayar da umurnin shugaba cewa, ya haramta bangaren soja na kungiyar Hamas. Manazarta suna ganin cewa, bunkasuwar al'amarin ya nuna cewa, Abbas zai yi watsi da kungiyar Hamas don neman samun wani rukuni daban.

Kafofin watsa labaru sun lura da cewa, a ran 16 ga wata, Abbas ya bayar da umunin shugaba na musmman domin kaucewa majalisar dokoki da kungiyar Hamas ke da kujeru masu rinjiya a yanzu, yayin da Salam Fayyad, firayim ministan gwamnatin gaggawa da ya nada zai kafa majalisar ministoci. Haka kuma gwamnatin gaggawa da aka kafa a ran 17 ga wata, za ta iya kula da gabar yammacin Kogin Jordan da zirin Gaza a duk fannoni bisa dokar ta baci da sauran dokoki, ta yadda Abbas zai kara samun damar ja-in-ja a tsakaninsa da kungiyar Hamas bisa son ransa.

Kafofin watsa labaru sun lura da cewa, bayan kafuwar gwamnatin gaggawa, nan da nan sai ta sami goyon baya daga wajen kasashen Amurka da Isra'ila da na Turai da yawancin kasashen Larabawa. Wasu kasashen yammaci da kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka taba kakkaba wa gwamnatin hadin kan al'ummar Falasdinu da ke karkashin shugabancin kungiyar Hamas takunkumi sun bayyana cewa, za su bai wa sabuwar gwamnatin Faladinu gudummuwa kai tsaye. Wannan yana nufin cewa, nan gaba ba ma kawai gwamnatin gaggawa za ta iya samun goyon baya daga bangarorin nan da abin ya shafa a fannin karfafa zuciya ba, har ma za ta sami gudummuwar kudi da na kayyyaki da sauransu. Sabo da haka halin da take ciki zai fi kungiyar Hamas wadda gamayyar kasa da kasa ke kakkawa mata takunkumi sosai.


1 2 3