Kauyen Juzhou wani kauye daban ne da ke fi nuna sigar musamman ta fuskar yawon shakatawa a Ji'an. Tilas ne mutane su je wajen ne cikin jiragen ruwa, saboda yana cikin wani karamin tsibiri mai suna Juzhou. Gasar tseren kwale-kwale da 'yan kauyen su kan shirya ta kan jawo hankulan kusan dukkan masu yawon shakatawa da ke ziyara a nan. An kera kwale-kwale bisa sifar Long, wato wata dabba ce a cikin almarar kasar Sin. Malam Gong Jianyu, wanda ya zo daga jihar Inner Mongolia da ke arewacin kasar Sin, ya ji farin ciki saboda shiga gasar tseren kwale-kwale, ya ce, 'Ban iya shiga irin wadannan ayyukan gona ba a babban fili mai ciyayi na jiharmu ta Inner Mongolia, musamman ma gasar tseren kwale-kwale, saboda haka, yau na ji farin ciki kwarai.'
A kauyen Juzhou, masu yawon shakatawa ba kawai su kan yi gwajin dashen shimkafa da haka kananan gorori da cire 'ya'yan itatuwa da sauran ayyukan gona ba, har ma su kan samu shiga bukukuwan rera wakoki da na nuna fitilu da sauran bukukuwan al'adun gargajiya masu ban sha'awa. 'Mike, ka zo ka taimake ni mu haka kananan gorori tare, Lina ta fi mu sauri. Kada ka kallo kawai, ka zo nan, saurayi. Wannan na da ban sha'awa sosai. Tabbas ne za ka son wannan wasa.'
1 2 3
|