Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-12 17:48:25    
Yin yawon shakatawa a kauyukan gundumar Ji'an ta lardin Jiangxi

cri

Yau za mu gabatar muku wata hanya daban da za ku bi in kuna son kara fahimtar kasar Sin, wato kai ziyara ga kauyuka, kauyukan da ke birnin Ji'an na lardin Jiangxi da ke tsakiyar kasar Sin su ne wurare masu kyau a gare ku. Saboda za ku iya noma da kanku da kuma shiga gasar tseren kwale-kwale iri na kasar Sin, sa'an nan kuma, za ku iya dandana abinci masu dadin ci kuma masu sigogin musamman da 'yan kauye suke samarwa. Ko kuna sha'awa? To, bari mu je wadannan kauyuka.

Kauyen Meipi ya fi shahara a Ji'an. Yana kudu maso gabashin Ji'an, fadinsa ya kai murabba'in kilomita daya kawai, amma yana da dogon tarihi na tsawon shekaru 800 ko fiye. Masu yawon shakatawa suna iya more idanunsu da wani irin wasan kwaikwayon musamman da 'yan kauyen su kan nuna a ko wace rana. Yara ne suke nuna wannan wasan kwaikwayo, sun sa tufafin wasan kwaikwayo da abin rufe fuska, sun yi kamar yadda mashahurai na tarihi da kuma mutanen da ke cikin wasannin kwaikwayo suka yi. An daure kafafun wadannan yara a kan katako, 'yan kauyen baligai sun daga wadannan katako, suna tafiya tare da kide-kide, yaran kuma sun nuna wasannin kwaikwayo a kan katakon. Madam Park Zung-shoo, wata 'yar kasar Korea ta Kudu, ta nuna babbar sha'awa kan irin wannan wasan kwaikwayo, ta ce, 'Ban yi tsammanin cewa, zan iya kallon wasan kwaikwayo mai ban sha'awa haka a Ji'an ba. Sa'an nan kuma, akwai tsoffin abubuwan al'adu na kasar Sin iri daban daban a nan, kamar su gidan tunawa da magabata da tsofaffin tituna. Na ga kauyen da aka gina a zamanin daular Ming da ta Qing na kasar Sin a nan, wanda ban taba ganin irinsa a da ba. Ina son wannan kauye sosai, zan gabatar da shi ga abokaina.'

An mayar da kauyen Meipi ya zama gidan nune-nunen tsoffin kauyuka na kudancin kasar Sin, saboda ya kasance da cikakkun gidajen kwana 503 da dakunan tunawa da magabata 19 da kwalejojin koyarwa na zamanin da da kuma tsofaffin abubuwan tunawa 8 wato Paifang a Sinance a nan. A arewancin kauyen, akwai wani titi mai tsawon shekaru dari 5 zuwa 6.

Masu yawon shakatawa sun fi son yin kwana a cikin wadannan tsofaffin gie-gine. A shekarar da muke ciki ne aka kafa wasu otel-otel irin na zamanin da a bayan kauyen Meipi, ta haka masu yawon shakatawa sun iya kai ziyara ga wadannan otel-otel da ke dab da kauyen, sa'an nan kuma, an iya kiyaye tsoffin gine-gine da ke cikin kauyen yadda ya kamta. Malam Liang Xingfa, dan kauyen Meipi, ya bayyana cewa, 'Gina otel-otel a bayan kauyenmu bisa hadadden tsarin da aka tsara. Wannan na amfanawa wajen kiyaye yadda tsohon kauyenmu yake, haka kuma yana ba da taimako wajen tafiyar da otel-otel.'

1 2 3