Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-08 11:58:31    
Ana bunkasa harkokin tattalin arzikin fadama a jihar Ningxia ta kasar Sin cikin kuzari

cri

A jihar Ningxia, yin yawon shakatawa a kan ruwa, da kiwon agwagwa da makamantu, da noman tsire-tsiren ruwa, da kiwon kifaye da sauran amfanin ruwa manyan sana'o'i ne da ake yi a kan ruwa. Bisa kyakkyawan sakamako da hukumar kula da harkokin kyautata sauruka ta jihar Ningxia ta samu, kananan hukumomin wurare daban daban na jihar suna nan suna tsara fasalin raya sana'o'in ruwa bisa halin da suke ciki. Malam Zao Yongbiao, shugaban hukumar kula da aikin noma da na kiwon dabbobi ta jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon aiwatar da harkokin kanta ya bayyana cewa, nan da 'yan shekaru masu zuwa, hukumomin jihar za su ba da babban taimako wajen bunkasa sana'o'in ruwa. Ya kara da cewa, "jiharmu tana da albarkatun ruwa mai armashi wajen bunkasa sana'o'in ruwa. A lokacin da jiharmu ke aiwatar da kasafinta na 11 na shekaru biyar na bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma, muna kokari sosai wajen bunkasa sana'o'in ruwa. Yanzu mun fara samun sakamako mai kyau wajen bunkasa sana'o'in nan. Bisa ci gaba da muke samu wajen kiwon kifaye, muna sayar da su masu yawa zuwa jihohin Tibet da Qinghai da Gansu da Shaanxi da sauransu wadanda ke makwabtaka da jiharmu. "

An ruwaito cewa, an fara samun sakamako mai kyau wajen gudanar da harkokin tattalin arzikin fadama a jihar Ningxia. Zuwa shekarar 2010, fadin fadamu na jihar nan zai kai kadada dubu 20 don gwada misali ga kiwon amfanin ruwa da agwagwa da makamatansu da noman tsire-tsiren ruwa da yawon shakatawa a kan ruwa da sauransu.(Halilu)


1 2 3