Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-08 11:58:31    
Ana bunkasa harkokin tattalin arzikin fadama a jihar Ningxia ta kasar Sin cikin kuzari

cri

Da aka tabo magana a kan jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon aiwatar da harkokin kanta da ke a arewa maso yammacin kasar Sin, mai yiwuwa ne, a farko mutane da yawa za su tuna da fari da ake yi a jihar da kuma hamada mai fadi. Amma a hakika dai, ruwan shahararren rawayen kogi na kasar Sin yana malala ta garuruwa da gundumomi 11 da ke a arewancin jihar nan, don haka ya kasance da albarkatun fadamu masu fadi a jihar. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ba ma kawai jihar Ningxia ta inganta kiyaye albarkatun ruwa da yin amfani da shi da kuma kyautata yanayin kasa a bayyane ba, har ma ta bunkasa harkokin tattalin arzikin fadama cikin kuzari.

Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin kyautata sauruka ta jihar Ningxia ta yi, an ce, a halin yanzu fadin fadamu ya wuce kadada dubu 21 a jihar. Malam Liu Jiding, shugaban ofishin kula da aikin ba tare da gurbacewar muhali ba na hukumar ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun nan da suka, jihar Ningxia ta inganta kiyaye albarkatun fadama. Ya kara da cewa, "a cikin shekarun nan da suka wuce, yayin da muke mai da hankali sosai ga farfado da fadamu, kuma muna yin amfani da su ta hanyar kimiyya kamar yadda ya kamata. Da farko, mu yi musu shinge , sa'an nan mu farfado da su. Yanzu, fadin ruwan fadamu jiharmu ya wuce kadada 6,600, kuma fadin fadamun marasa ruwa mai yawa ya wuce kadada 14,000. "


1 2 3