Daga baya, Mr. Jonas ya fayyace, cewa za a gudanar da wannan horaswa har zuwa watan Oktoba na shekarar da muke ciki. A duk tsawon lokacin, kungiyar wasan basketball na maza ta kasar Sin za ta halarci gasar tsakanin kasashe 4 da kuma gasar cin kofin Stankovic da za a gudanar a cikin gidan kasar bisa gayyata; Ban da wadannan kuma, za ta kai ziyara a wasu kasashen Turai da kuma kasar Amurka domin yin gasa tae da kungiyoyi masu karfi na duniya.
Dadin dadawa, Mr. Jonas ya jaddada, cewa idan kungiyar wasan basketball na maza ta kasar Sin tana so ta samu sakamako mai gamsarwa a cikin wadannan jerin gasanni ta yadda za ta kara imanin halartar taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, to dole ne ta yi shiri sosai da sosai tun da wuri.
A dakin horo, wakilinmu ya ga 'yan wasa maza na kungiyar kasar Sin sun nuna himma da kwazo wajen buga kwallo bisa jagorancin wani mai koyar da 'yan wasan daban wato Mr. Arvydas na kasar Lithuania, wanda kuma ya fadi, cewa ko shakka babu 'yan wasa na kasar Sin suna da wayo wajen buga kwallo. Ya kuma hakkake, cewa kungiyar wasan basketball na maza ta kasar Sin za ta iya cika gibin dake kasancewa tsakaninta da sauran kungiyoyi masu karfi na duniya.(Sani Wang) 1 2 3
|