Aminai 'yan Afrika, kuna sane da, cewa har kullum akan mayar da gasar wasan basketball na maza a matsayin daya daga cikiin gaggaruman ayyukan wasanni da suka fi janyo hankulan 'yan kallo a gun taron wasannin Olympic. Game da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 dai, kungiyar wasan basketball na maza ta kasar Sin tana cike da kyakkyawan fatan fid da gwani a bakin kofar gida.
Ko kuna sane da, cewa kungiyar wasan basketbal na maza ta kasar Sin dake hade da shahararren dan wasa mai tsaron tsakiya mafi nagarta na NBA wato Yao Ming ta taba shiga cikin jerin kungiyoyi masu karfi na wasan basketball na maza na taron wasannin Olympic na Aden da aka gudanar a shekarar 2004 a kasar Girka. Yanzu ta soma yin horaswa ta mataki na farko domin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.
Kwanakin baya ba da dadewa ba, an kaddamar da sunayen 'yan wasa 22 na kungiyar wasan basketball na maza ta kasar Sin. 5 daga cikinsu, sun hada da mashahurin dan wasa wato Yao Ming dake aiki a kungiyar wasan basketball ta Huston Rockets a kasar Amurka, da dan wasa mai suna Yi Jianlian dake shiga gasar zaben nagartattun 'yan wasa na NBA a wannan shekara da ake yi a kasar Amurka da kuma dan wasa mai tsaron tsakiya wato Wang Zhizhi, wanda kuma ya taba yin aiki a kungiyar waan basketball ta Dallar Mavericks ta kasar Amurka.
1 2 3
|