Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-08 11:56:23    
Kungiyar wasan basketball ta kasar Sin na yin horaswa a tsanake domin taron wasannin Olympic na Beijing

cri

Ko da yake wadannan mashahuran 'yan wasa ba su samu horon da ake yi a wannan gami saboda wasu dalilai ba, amma duk da haka, babban mai koyar da 'yan kungiyar kasar Sin wato Mr. Jonas Kazlauskas dan asalin kasar Lithuania ya ce ba ya damuwa da wannan. Yana cike da imanin cewa, yanzu Yao Ming yana cikin kyakkyawar hali na shiga gasannin wasan basketball na NBA a kasar Amurka; Ban da wannan kuma, dan wasa Yi Jianlian shi ma na shiga horaswa da sashen kula da harkokin NBA ya shirya; Game da dan wasa wato Wang Zhizhi dai, Mr. Jonas ya ce, ' ba na damuwa a kai domin shi wani nagartaccen dan wasa ne na sana'a, wanda yake san abin da ya kamata ya yi.'

Domin neman samun sakamako mai kyau a gun taron wasannin Olympic da za a gudanar a kofar gida, kungiyar wasan basketball na maza ta kasar Sin ta bada kwangila daukar Mr. Jonas Kazlauskas a matsayin babban mai koyar da kungiyar a shekarar 2005.

Ko kuna sane da, cewa Mr. Jonas ya shahara kwarai a dandalin wasan basketball na duniya, ya taba jan ragamar kungiyar kasar Lithuania ga cimma burin zama zakara a taron wasannin Olymmic na Atlanta a shekarar 1996; Ban da wannan kuma, ya yi alfaharin zama malamin koyarwa mafi nagarta na Turai a shekarar 2000. Hukumar kula da harkokin wasan basketball ta kasar Sin na sa ran samun taimako daga wajensa bisa ilmi da kuma fasahohin da yake da shi.

Mr. Jonas yana ganin, cewa idan an kwatanta da hadaddun gasannin wasan basketball dake bisa matsayin koli na duniya, to lallai an tafi an bar hadaddiyar gasa ta wasan basketball ta kasar Sin baya a fannin zafin horaswa da na gasa. " Idan kungiyar wasan basketbal na maza ta kasar Sin tana so ta sami maki mai kyau," in ji shi, "to, wajibi ne ta samu zazafan horo domin kara karfin jikuna".


1 2 3