Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-07 19:35:38    
Tsarin jarrabawar neman shiga jami'a yana taka rawa mai yakini a fannin fitar da kwararru a kasar Sin

cri

Illolin da tsarin nan ke da su sun kuma jawo hankalin gwamnatin kasar Sin. Sau tari ne jami'an ilmi na kasar Sin suka gabatar da hanyar da za a bi wajen gyaran jarrabawar, kuma suna yin gwaje-gwaje a kan me ya kamata a jarraba. Bayan haka, an kuma gabatar da wasu matakai masu tausayawa. Misali, da ma, a kan gudanar da jarrabawar a ranar 7 ga watan Yuli na ko wace shekara, amma yanzu, an gyara lokacin jarrabawar zuwa ranar 7 ga watan Yuni, don kawar da wahalar yanayin zafi da masu shiga jarrabawar ke sha. Bayan haka, an kuma janye kayyade shekarun masu shiga jarrabawar da aka taba yi. Wadannan matakai sun sami karbuwa kwarai da gaske. Xia Xueluan, shehun malami a jami'ar Peking, shi ma ya bayar da nasa shawara, ya ce,"kamata ya yi an hada sakamakon jarrabawar wani da yadda yake yi a kullum a makaranta, kada dai a dogara ga wata jarrabawa kawai. Sa'an nan, a hada sakamakon jarrabawar da ingancinsa a fannonin da'a da hikima da kuma lafiyar jiki gaba daya, a kara mai da hankali a kan fasahohin dalibai da kuma iyawarsu. A zabi 'yan makaranta da suke da nagarta a fannoni daban daban zuwa jami'o'i."(Lubabatu)


1 2 3