Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-07 19:35:38    
Tsarin jarrabawar neman shiga jami'a yana taka rawa mai yakini a fannin fitar da kwararru a kasar Sin

cri

Li Xiaonan, wadda ta shiga jarrabawar neman shiga jami'a a shekarar bara, yanzu tana karatu a jami'ar Peking, a ganinta, jarrabawar shiga jami'a tsari ne mai adalci, sabo da kowa na iya samun damar zurfafa ilminsa ta hanyar yin jarrabawar. ta ce,"jarrabawar shiga jami'a hanya ce mai kyau. Idan babu jarrabawar, mai yiwuwa ne da yanzu ina wani karamin aiki a can karamin garinmu, amma ga shi yanzu na kara samun dama, kuma burina ma ya girma."

Amma duk da haka, zaman al'ummar kasar Sin ya sami sauye-sauye kwarai da gaske a cikin shekarun nan 30 da suka wuce, kuma tattalin arzikin kasar ma ya bunkasa kwarai, kuma bukatun jama'a kan zurfafa ilminsu ma sai dinga karuwa yake yi. A cikin irin wannan hali ne, gyaran jarrabawar shiga jami'a yana kara jawo tunanin jama'a.

Wasu masanan ilmantarwa sun yi nuni da cewa, Sin tana da jama'a masu dimbin yawa, amma ga shi abubuwan taimaka wajen ba da ilmi suna da karanci, shi ya sa tsarin jarrabawar shiga jami'a ya dace da halin da kasar Sin ke ciki, amma duk da haka, ita ma ya haddasa wata matsala, wato jarrabawar ta kan tabbatar da makomar wani, ko da yake ya nuna adalci, amma yana kuma hura wa 'yan makaranta wuta. Bayan haka, daga wasu fannoni ne, wannan tsari tana kuma tsananta matsalar nan ta "ba da ilmi ne domin jarrabawa", wanda ba zai amfana wa dalibai da su karu daga dukan fannoni ba.


1 2 3