A yau ranar 7 ga wata, an soma yin jarrabawar neman shiga jami'a a nan kasar Sin, kuma 'yan makaranta miliyan 10 a wurare daban daban na kasar sun shiga jarrabawar. Yau shekaru 30 ke nan tun bayan da aka maido da tsarin yin jarrabawar shiga jami'a a kasar Sin, to, sai dai yaya ake ganin jarrabawar nan ta shiga jami'a? Kuma a yayin da zaman al'umma ke ta samun ci gaba, a wadanne fannoni ne ya kamata a gyara tsarin? To, yanzu sai a gyara zaman a saurari wani rahoton da wakilinmu ya turo mana dangane da jarrabawar.
A shekarar 1977, kasar Sin ta maido da yin jarrabawar neman shiga jami'a da aka katse ta har cikin wani guntun lokaci, kuma matasa 'yan makaranta sun sake samun damar zurfafa ilminsu bisa jarrabawar. Shiga jami'o'in da suke so ta hanyar jarrabawar buri ne da dimbin 'yan makaranta ke kokarin neman cimmawa, a yayin da jarrabawar ta kuma kasance wata muhimmiyar hanyar da jami'o'in ke bi wajen daukar dalibai. A cikin shekaru 30 da suka wuce, jarrabawar ta fitar da dimbin kwararru a kasar Sin, kuma tsarin nan ya sami karbuwa daga jama'a. Xia Xueluan, wani shehun malamin ilmin zaman al'umma a jami'ar Peking, ya ce,"A halin yanzu a kasar Sin, jarrabawar neman shiga jami'a hanya ce daya kawai da ake bi wajen fitar da kwararru cikin adalci, wanda kuma ke samun karbuwa daga jama'a. Tsarin yin jarrabawar shiga jami'a yana bayar da nasa taimako ta fuskar horar da dimbin 'yan kwadago iri iri, musamman ma kwararrun kimiyya da fasaha, haka kuma yana ba da taimako a wajen kara karfin kasa da kuma raya kasa irin na kimiyya da fasaha da na kirkire-kirkire.
1 2 3
|