Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-06 15:53:26    
M.D.D. ta nemi kasashe daban-daban da su dauki matakai domin magance sauye-sauyen yanayi

cri
 

Kan matsalar yaki da bala'o'in duniya, M.D.D. ta nemi kasashe daban-daban da su gudanar da abubuwan da aka gabatar cikin "Tsarin aikin Hyogo" da sauran muhimman yarjeniyoyin da abin ya shafa. A shekarar 2005 a gundumar Hyogo na kasar Japan, an kira taron yaki da bala'o'in duniya wanda M.D.D. ta shugabanta. Taron ya tsara shirin yaki da bala'o'in duniya cikin shekaru 10 masu zuwa, kuma ya tsaida muhimman tsare-tsare da ayyuka 5 da za a yi domin yakin da bala'o'in duniya daga shekarar 2005 zuwa ta 2015, wato su ne, a tabbatar da aikin yaki da bala'o'i ya daya daga cikin muhimman ayyukan sassan gwamnatocin kasashe daban-daban. A bambanta da kuma kimanta sa ido kan hadarurrukan halittu, da kara karfin ba da labarin yiwuwar aukuwar mummunan yanayi tun kafin lokaci. A mai da muhimmanci wajen samar da zaman lafiya da yaki da bala'o'i daga fannoni daban-daban.

Cikin jawabin da Mr. Holmes ya yi a gun taron ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu da akwai kasashe 168 na duniya wadanda suka yarda da wannan yarjejeniya, aikin da ke gaban kasashen duniya shi ne, sun gudanar da tsare-tsare daban-daban da ke cikin yarjejeniyar sosai. Sa'an nan ya bayyana cewa, ya kamata gwamnatoci su zama ginshikai wajen yin rigakafi da yaki da bala'o'i, muhimmin abu shi ne su zuba kudi domin wannan aiki, idan da ba a samu tabbaci wajen kudi ba, kome kyaun shiri ba zai kawo amfani ba. (Umaru)


1 2 3