Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-06 15:53:26    
M.D.D. ta nemi kasashe daban-daban da su dauki matakai domin magance sauye-sauyen yanayi

cri

A ran 5 ga watan Yuni, rana ce ta muhallin duniya, a wannan rana kuma M.D.D. ta kira taro a birnin Geneva domin yaki da bala'o'in duniya, a gun taron an tattauna sabon halin da ake ciki a kasashe daban-daban domin yaki da bala'o'i, da daukar matakai domin fuskantar kalubalen da aka kawo sakamakon karuwar dumamar yanayin duniya.

Jami'an hukumomin M.D.D. da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu, da kwararrun masana fasaha da wakilan gwamnatoci na kasashe fiye da 100 sun halarci wannan taro. Mr. John Holmes, mataimakin babban sakataren kula da harkokin ba da gudummawa na jin kai na M.D.D. ya yi jawabi kan babban take, inda ya bayyana cewa, bisa rahoton da hukumar M.D.D. ta bayar a farkon rabin shekarar nan kan yanayin watan Maris na wannan shekara an ce, yanayin duniya ya kara dumama, wannan ya riga ya zama wata tabbatacciyar magana bisa kimiyya, kada a yi shakku a kan wannan. Amma wannan hakikanin abu ya kara kawo aikin gaggawa ga tsarin kasa da kasa wajen yaki da bala'o'i. Dole ne a tashi tsaye nan da nan a nemi bakin zaren domin fuskantar kalubale iri daban-daban, da rage hasarar da bala'o'in za su haddasa, kuma a dauki muhimmin mataki domin kau da illar da aka kawo sakamakon sauye-sauyen yanayi.


1 2 3