Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-06 15:53:26    
M.D.D. ta nemi kasashe daban-daban da su dauki matakai domin magance sauye-sauyen yanayi

cri

Bisa shawarar da M.D.D. ta bayar an ce, ya kamata kasashe daban-daban su yi ayyuka daga fannoni 2 domin yin rigakafi da yaki da bala'o'i.

Na farko shi ne, a kara shimfida muhallin kwanciyar hankali wajen gidajen kwana, ta yadda za a magance hadarurrukan da bala'o'in halittu za su jawo. Bisa kididdigar da aka yi an ce, yawan mutanen duniya da suka sha bala'o'i ciki har da fari da mahaukaciyar iska da ambaliya a shekarar da ta wuce ya kai miliyan 134. M.D.D. ta nemi kasashe daban-daban da su mai da hankali a lokacin da suke yin fasalin biranensu, su yi la'akari da sauye-sauyen yanayi, ta yadda za su tabbatar da zaman lafiyar makarantu da gidajen kwana da unguwannin birane.

Na 2, ya kamata a kiyaye sakamakon dan adam da aka samu wajen tattalin arziki don kada a kwashe su sabo da bala'o'in halittu. An nuna wasu alkaluma cewa, yawan hasarar da aka sha kai tsaye sabo da bala'o'in halittu na duk duniya ya kai dala biliyan 35 a kowace shekara. M.D.D. ta nemi kasashe daban-daban da su kafa tsarin ba da labarin yiwuwar aukuwar mummunan yanayi tun kafin lokaci, da kara kiyaye muhimman gine-ginen da aka yi a bakin teku.


1 2 3