A watan Janairu na shekarar da ta gabata, wata shugaba mai ci Ellen Johnson Sirleaf ta kasar Liberia ta yi rantsuwar hau kujerar mulkin kasar, a farkon watan Maris na wannan shekara, sabuwar gwamnatin kasar Liberia ta gabatar da bukatarta na mayar da Taylor, bayan da kasar Nijeriya ta amince da bukatar, sai Taylor ya gudu a daren ranar 27 ga watan Maris na shekarar da ta gabata, a daren ranar 28 ga watan Maris na wannan shekara, rundunar sojojin tsaron kai ta kasar Nigeriya ta kama shi a wurin da ke tsakanin iyakar kasar Nijeriya da Kamaru, kuma an kai shi zuwa hedkwatgar kasar Liberia, sa'anan kuma gwamnatin Liberia ta mika shi ga Kotun Musamman ta Majalisar Dinkin Duniya ta kasar Saliyo.don kawar da rikicin da zai faru a kasar Saliyo, an kai Tailor zuwa birnin Hague don yi masa tuhuma. Sa'anan kuma, kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya ya zartas da kuduri na yi wa Taylor tuhuma a kotun musamman da ke birnin Hague.
Kafin wannan, Taylor ya musunta dukkan karar da aka yi masa, za a bin bahasin laifufukan Taylor a cikin watanni 18, kuma yawan masu ba da shaida zai kai 140. Idan an tabbatar da laifufukan da ya yi, to za a tsare shi cikin gidan aya har dukkan rayuwarsa a duniya.(Halima) 1 2 3
|