Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-05 15:22:22    
An soma tuhuma kan laifufukan da tsohon shugaban kasar Liberiya Charles Taylor ya yi a birnin Hague na kasar Netherland

cri

A ranar 4 ga wannan wata, a birnin Hague na kasar Netherland, kotun musamman ta Majalisar Dinkin Duniya ta kasar Saliyo ta soma tuhuma kan tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor bisa sanadiyar laifufukan da ya yi na tayar da yaki da yin adawa da 'yan Adam a cikin yakin basasa da aka yi a kasar Saliyo, wannan ne karo na farko da aka yi wa wani tsohon shugaban kasar Afrika tuhuma a kotun musamman ta Majalisar dinkin Duniya.

A ranar da aka fara saurarar shari'ar, Taylor bai fito a Kotun ba. A cikin wata wasikarsa da ya dora wa lauyarsa nauyin karantawa , ya bayyana cewa, dalilin da ya sa bai fito a kotun ba shi ne saboda ba shi da kwarin guiwa sosai ga yadda kotun ke aiwatar da dokokin shari'a bisa adalci. Lauyar da ya karanta wasikar Mr Karim Khan ya wakilci Taylor wajen halartar tuhumar da ake yi wa Taylor. Amma Mr Karim Khan ya bayyana cewa, Taylor ya riga ya tube shi, kuma shi kansa ya dauki nauyin lauya don kare shi kansa kawai, saboda haka Karim Khan ya janye jikinsa daga Kotun ba tare da bata lokaci ba. A kotun da ake saurarar shari'ar  , babban alkali malama Julia Sebutinde ta dorawa wani mutum nauyin kare shi , saboda haka ana ci gaba da tuhumar a kotun.


1 2 3