Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-05 15:22:22    
An soma tuhuma kan laifufukan da tsohon shugaban kasar Liberiya Charles Taylor ya yi a birnin Hague na kasar Netherland

cri

Mun sami labari cewa, Taylor ya hau kujerar mulkin kasarsa a shekarar 1997,a duk tsawon lokacin da yake rike mulkin kasar, ya yi iyakacin kokari don nuna goyon baya ga hadadiyyar kungiyar fafifikar juyin juya hali wato dakaru masu yin adawa da gwamnati, ta hanyar damar nan ne ya sarrafa albarkatan ma'adinan kasar Saliyo , musamman ma ga ma'adinan Lu'u-lu'u wato diamond cikin Turanci, a sa'I daya kuma, ta hanyar kawo wa gwamnatin Saliyo rikici ne ya kara habaka tasirinsa a shiyyar yammacin Afrika. Hadadiyyar kungiyar fafifikar juyin juya hali ta yi amfani da makaman da Taylor ya samar mata a wajen haddasa mummunan rikici a kasar Saliyo.

A watan Maris na shekarar 2003, Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta kasar Saliyo ta yi wa Taylor tuhuma bisa laifin tayar da yaki da cin zarafin bil  adam a cikin yakin basasa da aka yi a kasar saliyo, sa'anan kuma kotun ta bayar da umurnin kama shi,inda aka nemi kungiyar 'yan sandan kasashen duniya da su ba da taimakon kama shi. a watan Augusta na wannan shekara, don kawo karshen yakin basasa da aka yi a kasar Saliyo cikin shekaru 14, kungiyar tarayyar tattalin arziki ta kasashen yammacin Afrika ta samar wa Taylor makafar siyasa a kasar Nijeriya. Sa'anna kuma, ba sau daya ba ba sau biyu ba Kotun Majalisar dinkin duniya ta kasar Saliyo ta nemi gwamnatin Nijeriya da ta kai Taylor zuwa Kotun don yi masa tuhuma, amma gwamnatin Nijeriya ta bayyana sosai cewa, muddin kasar Liberia ta kafa gwamnatin farar hula da kuma ta gabatar wa kasar Nijeriya bukatar da abin ya shafa, to gwamnatin Nijeriya za ta mayar da Taylor zuwa kasar Liberia.


1 2 3