Wurin kiyaye abubuwan al'adun kabilar Dong na Tang'an shi ne wani wurin kiyaye abubuwan al'adu daban a Guizhou. 'Yan kabilar Dong sun yi shekaru 700 ko fiye suna zaune a kauyen Tang'an. Kauyen Tang'an na dab da kungurmin daji, ana iya samun tsofaffin abubuwan halitta masu dimbin yawa a nan. Game da sigar musamman da kauyen Tang'an ke da ita ta fuskar gine-gine, malam Wang Jun, wanda ke jagorantar mu, ya yi bayanin cewa,
'A tsakiyar kauyen, akwai wani irin ginin da ya fi gargajiya, wato hasumiyar musamman. 'Yan kabilar Dong su ne suka gina ta da kansu, wanda ba a taba ganin irinta a sauran wurare ba. A can da an yi amfani da ita don yaki da abokan gaba. Amma yanzu an yi mata sauye-sauye, ta zama wani wurin da tsoffi su kan yi wasan dara irin na kasar Sin, sa'an nan kuma, matasa su kan hira ko rera waka don nuna wa juna soyayya.'
A bakin kofar kauyen Tang'an, ana iya ganin filayen gona da 'yan kabilar Dong suka yi shekaru daruruwa suna kokarin samar da su a kan gangarar tsauni. A duk shekara, wadannan filayen gona sun sanya masu yawon shakatawa ba su son komawa gida. Wata jami'ar hukumar lardin Guizhou madam Long Chaoyun ta bayyana cewa,
'Yanzu idan masu yawon shakatawa suka kai wa kauyukanmu ziyara, 'yan kauyukan ba kawai sun iya harsunan kabilunsu ba, har ma sun iya harsunan waje, suna iya yin magana da bakinmu na kasashen waje.'(Tasallah) 1 2 3
|