Yanzu kananan kabilu 48 suna zama a lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Saboda ya kasance da kananan kabilu masu yawan haka, shi ya sa hukumar lardin ta ware wuraren ajiye abubuwan gargajiya 4 marasa ganuwa, don nuna wa masu yawon shakatawa na gida da na waje al'adun musamman da na gargajiya da wadannan kananan kabilu suke da su. Yau ma za mu kai ziyara ga wadannan wuraren ajiye abubuwan gargajiya na musamman a Guizhou.
Wadannan wuraren ajiye abubuwan gargajiya na musamman 4 su ne shiyyoyin kiyaye al'adun kananan kabilu, ko wanensu wani kauye ne da 'yan wata karamar kabila suke zama, ba a kafa dakunan musamman don yin nune-nune, ko nuna kayayyaki ba a nan, masu yawon shakatawa suna iya ziyara a kauyukan, inda suke iya kara fahimtarsu kan al'adun gargajiya da al'ada da gine-gine na kananan kabilu na wurin. Game da wadannan shiyyoyin kiyaye al'adun kananan kabilu da ke Guizhou, malam Wang Jun, wanda ya yi shekaru da dama yana aikin jagorar masu yawon shakatawa, ya bayyana cewa,
'An kafa shiyyoyin kiyaye al'adun kananan kabilu 4 a Guizhou, kasashen Sin da Norway sun hada gwiwa wajen kafa shiyya ta farko a yammacin Guizhou don kiyaye al'adun kabilar Miao, an kafa ta biyu a kudu maso gabashin Guizhou don kare al'adun kabilar Dong, a kudancin lardin kuma, akwai wata daban don kare al'adun kabilar Buyi, a kudu maso gabashin lardin ya kasance da wani tsohon gari mai suna Longli.'
1 2 3
|