Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-05 15:17:54    
Kabilun lardin Guizhou na kokarin kiyaye yanayi mai daukar sauti

cri

Hukumar lardin Guizhou da hukumomin kasar Norway da abin ya shafa sun hada kansu sun kafa wurin kiyaye abubuwan al'adun kabilar Miao na Suoga a kauyen da 'yan kabilar Miao ke zama a shekara ta 1998. 'Yan kabilar Miao fiye da dubu 4 suna zama a cikin kauyensu mai fadin murabba'in kilomita 120, wato wurin ajiye abubuwan al'adun kabilar Miao. Kawo yanzu dai 'yan kabilar Miao suna gadon al'ada mai dogon tarihi da kuma sigar musamman tasu a nan. Malam Xu Meilin, shugaban wannan wurin ajiye abubuwan al'adun kabilar Miao, ya yi karin bayani cewa,

'Wurin ajiye abubuwan al'adu namu ya zama na farko a duk kasar Sin har ma a duk Asiya, inda a galibi dai ba a canza al'adun gargajiya ba. Mutane suna zama da samun albarka ta hanyoyin gargajiya, haka kuma suna gadon fasahar rini, suna rawa da kide-kide ta hanyoyin gargajiya da na musamman, tufafi da abubuwan ado da suka sa sun fi jawo hankulan saura, saboda ba a iya ganin irinsu a sauran wuraren duniya ba.'

Idan masu yawon shakatawa sun kai wa kauyen Suoga ziyara, to, suna iya kallon yadda 'yan kabilar Miao suke dinka tufafinsu da hannunsu. Ban da kai ziyara ga wuraren da 'yan kabilar Miao ke zama da sa tufafinsu da yin wasa da abubuwan kida na gargajiya da yin amfani da abubuwan zaman yau da kullum da na aikin kawo albarka da kansu, masu yawon shakatawa suna iya daukar wadannan abubuwan tarihi na al'ada masu kyau ta hanyoyin daukar murya da bidiyo.


1 2 3