Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-25 13:02:36    
Lardin Anhui na kasar Sin na bunkasa aikin masana'antun kera motoci cikin sauri kuma tare da ikon mallakar fasaharsa

cri

Hukumomi na mataki daban daban na lardin Anhui sun dauki matakai da dama don tallafawa kamfanonin kera motoci na Jianghuai da Chery da sauransu wajen kera motoci bisa ikonsu na mallakar ilmi. Malam Zhang Jian, mataimakin shugaban hukumar kasuwanci ta lardin Anhui ya bayyana cewa, yayin da ake nacewa ga bin manufar kera motoci bisa ikon mallakar ilmi, gwamnatin lardin Anhui ma tana bai wa kamfanonin kera motoci kwarin guiwa wajen yin hadin kansu da kasashen waje a fannin fasaha. Ya kara da cewa, "yayin da ake kera motoci bisa ikon mallakar ilmi, wajibi ne, a yi musanye-musanye tare da kasashen waje, muna maraba da 'yan kasawa da su zo lardin Anhui su zuba jari. Wasu masaya da suka fito daga Amurka da kasashen Turai sun riga sun nuna burinsu na inganta hadin kansu da mu wajen binciken wasu samfurorin motoci da kuma kera su. Hukumarsa za ta kara samar da labaru da kyau ga kamfanonin kera motoci ta yadda za ta kara sa kaimi gare su don yin hadin kansu da kasashen waje."(Halilu)


1 2 3