Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-25 13:02:36    
Lardin Anhui na kasar Sin na bunkasa aikin masana'antun kera motoci cikin sauri kuma tare da ikon mallakar fasaharsa

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta kokarta sosai wajen bunkasa aikin masana'antun kera motoci, musamman ma tana mai da hankali sosai wajen bunkasa aikin masana'antun kera motoci tare da samun ikon mallakar fasaharta. Yanzu, lardin Anhui na kasar Sin ya kasance cikin sahun gaba wajen kera motoci tare da samun ikon mallakar fasaharsa.

Kamfanin kera motoci mai suna "Jianghuai" na lardin Anhui ya kafu ne a shekarar 1999. Yanzu, yawan motoci da yake fitarwa ya wuce dubu 200 a ko wace shekara. Yawancinsu kuma motocin daukar kaya da motocin 'yan kasuwa ne. Tun daga farkon lokacin kafuwarsa, kamfanin yana ta kokari sosai wajen kera motoci tare da samun ikon mallakar ilminsa. Yanzu, ba ma kawai kamfanin yana sayar da motocinsa a gida ba, har ma yana fitar da su zuwa kasashen kudu maso gabashin Asiya da kudancin nahiyar Amurka da kuma Afrika. Malam Wang Dongsheng, wani jami'in kamfanin ya bayyana cewa, "ta hanyar kafa cibiyar nazarin motoci a kasashen duniya, kamfaninmu yana samun fasahar ci gaba ta duniya da kwararru da kuma hadin guiwa wajen binciken motoci da kera su. Cibiyarmu a kasar Italiya ta dauki wasu kwararru na kasar don yin binciken, wani sabon samfurin mota da kamfaninmu zai fitar, cibiyar nan ita ce ta tsara fasalinta."


1 2 3