Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-25 13:02:36    
Lardin Anhui na kasar Sin na bunkasa aikin masana'antun kera motoci cikin sauri kuma tare da ikon mallakar fasaharsa

cri

A lardin Anhui, akwai wani babban kamfanin kera motoci daban da ake kira "Chery". Kamfanin shi ma yana kera motoci bisa ikonsa na mallakar ilmi. Yawan motoci da ya fitar ya wuce dubu 300 a shekarar bara. Ya fitar da motocinsa zuwa kasashe da yankuna da yawansu ya wuce 50. Ya kai matsayi na farko a kasar Sin wajen fitar da motoci zuwa kasashen waje. Malam Jin Yibo, kakakin kamfanin ya bayyana cewa, wani babban dalilin da ya sa kamfaninsa ya iya samun kyakkyawan sakamako kamar haka, shi ne domin nacewa ga aiwatar da manyan tsare-tsaren samun ikon mallakar fasaharsa. Ya kara da cewa, "ta hanyar kirkirawa, kamfaninsa ya kware wajen binciken motocinsa da kuma kera su, yanzu, yawan samfurorin motoci da yake fitarwa ya kai 8, haka kuma zai fitar da sabbin samfurorin motoci guda 6 a shekarar nan. Nan gaba ba da dadewa ba, Kamfanin Chery zai zama daya daga cikin kamfanonin kasar Sin da ke kera samfurorin motoci mafiya yawa. Ta haka za mu iya sayar da motoci masu samfurori daban daban zuwa kasuwanin iri-iri don biya bukatu da ake yi, yawan motoci da muke sayarwa zai kara samun kason motoci da ake sayarwa a kasuwanni. Mun iya samun irin wannan sakamako ne sabo da muna nacewa ga binciken ilmin motoci da kuma kera su."


1 2 3