Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-23 15:42:29    
Firayin minista na farko na kasar Sin

cri

Tun daga tsakiyar shekaru 50 zuwa tsakiyar shekaru 60 na karnin da ya gabata, bi da bi ne firayin minista Zhou Enlai ya kai ziyara a kasashe da yawa na Afirka da Asiya da kuma Turai, wadannan ziyarce ziyarce sun kara sada zumunci a tsakanin Sin da kasashen.

Daga ranar 14 ga watan Disamba na shekarar 1963 zuwa ranar 4 ga watan Faburairu na shekarar 1964, firayin ministan kasar Sin Zhou Enlai ya kai ziyarar aiki a kasashe 10 na Afirka, wadanda suka hada da Massar da Aljeriya da Morocco da Tunisiya da Ghana da Mali da Guinea da Sudan da Habasha da Somali. A lokacin ziyararsa, firayin minista Zhou ya gana da shugabannin kasashen 10 bi da bi, kuma ya gabatar da ka'idar sada zumunta a tsakanin kasashen Sin da Afirka. Wannan ya zama karo na farko ne da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a Afirka.

A shekarar 1965, firayin ministan kasar Sin Zhou Enlai ya kai ziyarar aiki a kasashe uku na Afirka wato Aljeriya da Massar da kuma Tanzaniya.

A ranar 8 ga watan Janairu na shekarar 1976, firayin ministan kasar Sin Zhou Enlai ya riga mu gidan gaskiya. Jama'ar kasar Sin sun yi bakin ciki sosai, sun yi zaman makoki cikin dogon lokaci domin rasuwar Zhou. Kwamitin sulhu na MDD kuma ya shirya bikin nuna ta'aziyya ga rasuwar Zhou, haka kuma ya saukar da tuta zuwa rabin sanda don yin ta'aziyya ga rasuwar Zhou.

To, jama'a masu sauraro, wannan shi ne bayani da muka kawo muku game da takaitacen bayani a kan firayin minista na farko na kasar Sin. Wannan kuma ya kawo karshen shirinmu na yau na "amsoshin wasikunku".(Danladi)


1 2 3