Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-23 15:42:29    
Firayin minista na farko na kasar Sin

cri

To, jama'a masu sauraro, a cikin zaurenmu na "amsoshin wasikunku", bari mu amsa wata tambaya da Malam Sanusi Isah ya rubuta mana, a cikin wakarsa, inda ya yi tambaya cewa, wane ne farkon firayin ministan kasar Sin?

Mr Zhou Enlai shi ne firayin minista na farko na kasar Sin. Mr Zhou kuma ya taba gudanar da manyan ayyuka da yawa a kasasr Sin, haka kuma ya taba sheda muhimman lamuran da yawa, wadanda suka da ma'anar tarihi. Firayin minista Zhou Enlai ya bautawa jama'ar kasar Sin cikin sahihiyar zuciya. To, jama'a masu sauraro, bari mu ga wasu bayanai dangane da shi.

An haifi Mr Zhou ne a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 1898 a birnin Huai'an da ke lardin Jiangsu na kasar Sin. A lokacin bazara na shekarar 1910, ya bar gida da kawunsa, sa'an nan kuma ya yi karatu a biranen Tieling da kuma Shenyang na lardin Liaoning na kasar Sin. A watan Agusta na shekara 1913, Mr Zhou Enlai ya shiga cikin jami'ar Nankai ta birnin Tianjin. Bayan haka kuma, ya gama karatu a wannan jami'a a watan Yuni na shekarar 1917.

Mr Zhou Enlai ya shiga cikin kungiyar kwaminis a birnin Paris, wadda ta taka wata muhimmiyar rawa wajen kafa jam'iyyar kwaminis ta Sin. A watan Faburari na shekarar 1923, Mr Zhou ya zama sakatare na reshen kungiyar matasa ta kwaminis ta Sin da ke kasashen Turai.


1 2 3