Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-23 15:42:29    
Firayin minista na farko na kasar Sin

cri

A watan Oktoba na shekarar 1934, Mr Zhou ya shiga cikin rukunin shugabannin jar rundunar sojoji a yayin da suke duguwar tafiya. A watan Janairu na shekarar 1935, Zhou Enlai ya halarci babban taro na Ofishin siyasa na tsakiyar Jam'iyyar kwaminis ta Sin a birnin Zunyi da ke lardin Guizhou, kuma ya nuna goyon bayansa ga Mao Zedong, wanda ya zama shugaba na farko na kasar Sin. Wannan taro yana da muhimmiyar ma'ana a tarihi, bayan haka, Mao Zedong da Zhou Enlai sun shugabanci jar rundunar sojoji domin su ci gaba da tafiya har lokacin da suka samu nasara a watan Oktoba na shekarar 1935.

A ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, an shirya babban bikin kafuwar sabuwar kasar Sin. Mr Zhou Enlai kuma ya halarci bikin, inda a nan ne aka nada shi a matsayin firayin ministan kasar Sin kuma ministan harkokin waje na kasar Sin. Bayan haka kuma, ya zama mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, da kuma mataimakin shugaban hukumar soja ta jama'ar kasar Sin. A watan Janairu na shekarar 1953, Mr Zhou Enlai ya shiga cikin aikin kafa dokar kundin tsarin mulki da kuma dokar zabe ta kasar Sin.

A watan Disamba na shekarar 1953, a karo na farko kuma a madadin kasar Sin, Mr Zhou Enlai ya gabatar da ka'idoji biyar wajen samun zaman lafiya da zaman tare wato girmama juna a harkar mulkin kai da cikakken yankin kasa, da rashin kai wa juna hari da rashin tsoma baki cikin harkokin gida na juna, da kuma yin zama daidai wa daida da moriyar juna da kuma yin zaman tare cikin lumana. To, wadannan ka'idoji biyar sun zama babban tushe ne da sabuwar kasar Sin take lura da su a dangantakar da ke tsakaninta da kasashen waje, haka kuma sannu a hankali sun zama ka'idojin da sauran kasashen duniya ke bi a yayin da suke harka da kasashen waje.

A shekarar 1954 da kuma 1955, firayin minista Zhou Enlai ya shugabanci tawagar kasar Sin domin halartar taron Geneva da na Bandung. Wannan shi ne a karo na farko da sabuwar kasar Sin ta shiga cikin manyan tarurrrukan duniya. Firayin minista Zhou ya nuna kwarewarsa sosai, sabo da haka ya samu yabo daga kasashen duniya, an mayar da shi 'dan diplomasiyya mafi kwarewa a duniya na lokacin.


1 2 3