Bisa matsayinsa na daya daga cikin wandanda suka tsara wannan shirin ba da taimako ga yankuna masu fama da talauci a fannin ayyukan koyarwa, Qing Guangya ya nuna gamsuwa sosai ga sakamako mai kyau da aka samu a cikin wannan aiki. Kuma ya bayyana cewa, wannan kwas din horaswa wata sabuwar jarrabawa ce, wanda ya shaida cewa, ana sa kaimi ga samun ilmi cikin daidaito. Haka kuma wannan aiki zai taka muhimmiyar rawa ga kyautata halin ba da ilmi da yankuna masu fama da talauci na lardin Sichuan ke ciki yanzu. Kuma ya kara da cewa,
"A kan fadi cewa, yankin da ke yammacin kasar Sin yana baya idan an kwatanta shi da yankin da ke gabashin kasar, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da muhimman ayyuka na yankin ba su da kyau. Kuma kauyukan da ke yammacin kasar Sin sun fi baya baya, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ya kasance da abubuwan da aka gaza yi wajen ayyukan koyarwa. Shi ya sa ina ganin cewa, aikin horar da malamai kai tsaye yana da muhimmanci, kuma aikin horar da malaman kauyuka yana gaban kome."
Ban da wannan kuma Mr. Qing ya yi zaton cewa, ko wace malamar da ta shiga kwas din horaswa za ta kai wa dalibai 500 alheri. Sabo da haka bayan shekaru da dama masu zuwa, tabbas ne matsayin ayyukan koyarwa na yankuna masu fama da talauci na lardin Sichuan zai taka wani babban mataki.(Kande Gao) 1 2 3
|