Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-21 15:19:11    
An fara horar da malamai mata na kauyuka a lardin Sichuan ta Sin

cri

Ko da yake a kan yi wannan kwas din horaswa har shekara guda kawai, amma kwarewar malaman da suka shiga kwas din horaswa wajen aiki ta samu ci gaba sosai. Kemucuo ita ce wata 'yar kabilar Tibet, har kullum tana yin ayyukan koyarwa a cikin wata makarantar firamare ta shiyyar kabilar Tibet mai cin gashin kai ta lardin Sichuan. A da, ba ta iya fadi Sinanci kamar yadda ya kamata ba balle ma harshen turanci. Amma bayan da ta shiga wannan kwas din horaswa, yanzu Kemucuo ta riga ta iya yin hira tare da malaman baki da turanci. Kuma ta gaya mana cewa,

"A da, makin da na samu wajen harshen turanci yana kasa kasa, amma yanzu na riga na iya yin hira tare da malamina da turanci."

A cikin wadannan malamai mata da suka shiga irin wannan kwas din horaswa, da yawa daga cikinsu sun riga sun zama kusoshi na makarantun da suke ciki, har ma wasu daga cikinsu sun samu lambobin yabo da a kan bai wa nagartattun malamai. Bisa labarin da muka samu, an ce, malamai biyu daga cikinsu sun zama kusoshin malamai na lardin Sichuan, haka kuma an gabatar da wata malama daga cikinsu zuwa kasashen wajen domin kara ilminta har shekara guda.

Ba a iya raba sakamako mai kyau da malamai mata na kauyukan kasar Sin suka samu tare da dabarun koyarwa na musamman da kwararrun gida da na waje a fannin ayyukan koyarwa suka dauka. Malamai mata da suka shiga kwas din horawa sun bayyana cewa, ba kawai sun samu ilmin ayyukan koyarwa ba, har ma abu mafi muhimmanci shi ne sun samu sabbin ra'ayoyin zamani wajen ayyukan koyarwa.


1 2 3