Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-21 15:19:11    
An fara horar da malamai mata na kauyuka a lardin Sichuan ta Sin

cri

Sabo da ba a iya bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin cikin daidaito kamar yadda ya kamata, shi ya sa har kullum yankunan kauyukan kasar Sin suke fuskantar yanayin karatu maras kyau da kuma karancin malamai masu kwarewar aiki sosai. Domin yaran da ke kauyaka suna iya samun ilmi kamar yaran da ke birane, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin tana karfafa kwarin gwiwar malamai masu kwarewar aiki wajen zuwan kauyuka don yin ayyukan koyarwa, da kuma shirya harkoki iri daban daban wajen horar da malaman kauyuka. Ban da wannan kuma ta tsara wani shiri, wato ya zuwa shekara ta 2010, kusan rabin malaman kauyuka da ke yankunan da ke tsakiya da yammacin kasar Sin za su iya samu kwas din horaswa. To, a cikin shirinmu na yau, za mu leka wani kwas din horaswa da aka yi wa malamai mata na kauyuka a lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin.

Masu sauraro, wannan murya ce ta malamai mata fiye da 30 na makarantun kauyukan lardin Sichuan wadanda suke shiga kwas din horaswa da kwararrun baki suka ba su a fannin harshen turanci. Suna bin malaminsu wajen karanta kalmomin turanci a tsanake.

An fara gudanar da wannan kwas din horaswa domin malamai mata na kauyuka ne daga shekara ta 2003. A ko wace shekara, malamai mata kusan 30 da suka zo daga yankuna masu fama da talauci na lardin suna iya shiga irin wannan kwas din horaswa na tsawon shekara guda ba tare da biyan kudi ba. Haka kuma a tsawon lokacin kwas din horaswa, kwararrun gida da na waje a fannin ayyukan koyarwa za su ba su darusa iri daban daban, ciki har da turanci, da na'urar kwamfuta, da dabarun ba da ilmi, da kuma ilmin tunanin dan Adam a fannin ayyukan koyarwa da dai sauransu. Ya zuwa yanzu, malamai mata fiye da dari na kauyukan lardin Sichuan sun riga sun shiga irin wannan kwas din horaswa.


1 2 3