Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-21 15:11:25    
Takaitaccen bayani gama da kabilar Yugu

cri

Ko da yake harufan kabilar Yugu ya riga ya bace, amma har yanzu ya kasance da nagartattun al'adun gargajiya na kabilar, ciki har da tatsuniyoyi da almara da wakokin jama'a da karin magana. Musamman wakokin jama'a na kabilar suna da halayen musamman. Galibin irin wadannan wakokin jama'a suna bayyana yadda 'yan kabilar suke aiki da neman soyayya. Waka mai suna "Huang Daicheng" da waka mai suna "Sanamako" sun fi suna a yankunan kabilar. Kowane dan kabilar Yugu ya iya rera wadannan wakoki biyu. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, masana na gida da na ketare sun yi nazari kan wakokin jama'a na kabilar Yugu, an kuma gano cewa, launin wasu wakokin barci na jarirai launi ne da kakanin-kakaninsu suka taba yin amfani da shi yau da shekaru dubu 2 da suka wuce.

Abincin da 'yan kabilar Yugu suke ci yana da nasaba da sana'arsu. Su kan sha shanyi na madara har sau 3 a kowace rana tare da shinkafa sau daya. Muhimman abincin da suke ci suna kunshe da shinkafa da garin alkama da sauran hatsi iri iri tare da madara da nama.


1 2 3