Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-21 15:11:25    
Takaitaccen bayani gama da kabilar Yugu

cri

Mutanen da yawansu ya kai kusan kashi 90 daga cikin kashi dari na duk yawan 'yan kabilar Yugu suna zama ne a gundumar Sunan ta kabilar Yugu mai cin gashin kanta ta lardin Gansu. Sauransu suna zama a wani kauyen birnin Jiuquan na lardin. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000 a duk fadin kasar Sin, yawan mutanen kabilar Yugu ya kai dubu 13 da 719. Kabilar Yugu ba ta da haruffa, suna amfani ne da harufan Sinanci.

A da, 'yan kabilar Yugu sun dogara ne da tattalin arziki ciki har da sana'ar kiwo da ta aikin gona na masu zaman kansu. Bayan kafuwar Jumhuriyar Jama'ar Sin, 'yan kabilar Yugu sun samu ikon zaman daidai wa daida da sauran kabilun kasar Sin cikin lumana da ikon mulkin yankinsu. A shekarar 1954, an kafa gundumar Sunan ta kabilar Yugu mai cin gashin kanta. A cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce, tattalin arziki da zaman al'umma da al'adu na yankunan kabilar Yugu sun sami cigaba sosai. A da, babu masana'antu a yankunan kabilar, amma yanzu an riga an gina masana'antu iri iri da kafa makarantun firamare da na sakandare da asibitoci da dakunan likitanci a yankunan kabilar domin tabbatar da samar wa jama'ar kabilar Yugu ilmi da harkokin kiwo lafiya. Sabo da haka, ingancin zaman rayuwar jama'ar kabilar ya samu kyautatuwa sosai.


1 2 3