Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 17:16:59    
Kasar Sin za ta kafa tsarin dashen gabobin jikin mutum nan da shekaru uku zuwa biyar masu zuwa

cri

Sa'annan Mr. Huang Jiefu ya bayyana, cewa da yake ana karancin gabobin jikin mutum, shi ya sa aka tanadi, cewa wajibi ne mutuwar kwayoyin kwakwalwa na mutum ta samu amincewa daga al'ummar kasar. Ya furta cewa: " Sai dai an amince da doka kan mutuwar gabobin jikin mutum ne kawai za a iya tabbatar da cewa bada gabobin jikin mutum da ake yi na da ma'anar gaskiya" domin a cewarsa gabobin jikin mutum za su zama abin banza cikin mintoci kadan bayan mutuwar mutum.

A karshe dai, Mr. Huang Jiefu ya jaddada, cewa da yake yawan kudin da akan kashe wajen dashen gabobin jikin mutum a kasar Sin ya fi na ketare araha, shi ya sa wasu mutane daga ketare sukan zo nan kasar Sin domin dashen gabobin jikin mutum. Lallai wannan ya saba wa ka'idojin da abin ya shafa na kungiyar WHO. Mr. Huang ya fadi cewa:

" Saboda ba a kashe kudade da yawa wajen dashen gabobin jikin mutum a kasar Sin, don haka, mutane da dama na ketare sukan zo nan kasar Sin domin dashen gabobin jikin mutum. Yanzu, mun yi watsi da wannan bisa manufa ban da 'yan-uwa na yankin Hongkong da Macao da kuma na Taiwan". ( Sani Wang )


1 2 3