Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 17:16:59    
Kasar Sin za ta kafa tsarin dashen gabobin jikin mutum nan da shekaru uku zuwa biyar masu zuwa

cri

An labarta, cewa kwanakin baya ba da jimawa ba, mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin Mr. Huang Jiefu ya karbi ziyarar da kafofin watsa labaru suka yi masa, inda ya furta, cewa takardar " Ka'idoji kan harkokin dashen gabobin jikin mutum" da gwamnatin kasar Sin ta kaddamar a hukumance a ran 1 ga watan Mayu da ya gabata tana da muhimmiyar ma'ana irin ta abun inshara ga kasar Sin. Amma, ya kasance da ayyuka da dama da za a yi wajen gudanar da takardar ka'idojin. Ana kyautata zaton cewa, kasar Sin za ta kafa tsarin dashen gabobin jikin mutum nan da shekaru uku zuwa biyar masu zuwa.

Jama'a masu saurare, ko kuna sane da, cewa kasar Sin ta fara dashen gabobin jikin mutum ne a shekarar 1960 na karnin da ya gabata. Kuma ta cimma tudun dafawa wajen bunkasa wannan sana'a cikin shekaru sama da goma da suka shige. Amma duk da haka, kasar Sin ta gamu da wasu matsaloli da yawa na rashin daidaitawar matsayin fasahohi, da karancin wadanda suka so su bada gabobin jikinsu da kuma gazawar hukumomin jiyya wajen aiki da dai sauransu a fannin dashen gabobin jikin mutum.

Domin canza wannan hali, kasar Sin ta fito da takardar " ka'idoji kan harkokin dashen gabobin jikin mutum". Mr. Huang Jiefu ya furta, cewa: "Harkokin dashen gabobin jikin dan adam na kunshe da tsare-tsare biyu, wato daya shi ne tsarin yin rajista ta hanyar kimiyya wato ke nan wadanne gabobin jikin mutum ake iya dashensu kuma wadanne majiyyata ne ake iya musu dashen gabobin jikin mutum; Daya daban shi ne tsarin yin rajista ta hanyar hukumar gwamnati, wanda yake kunshe da masoman samun gabobin jikin mutum, da ayyukan bada gabobin jikin mutum da kuma na rarraba su da dai sauransu."


1 2 3