Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 16:14:00    
Ma Yupeng, wani likita na kauyen kasar Sin

cri

Bayan da Ma Yupeng ya sauke karatu daga kwas din horaswa kan aikin likitanci, ya koma kauyen Dongtang domin zama wani likita, da kuma kula da ayyukan jiyya da kiwon lafiya na mazauna fiye da 300 na kauyen Dongtang da kuma sauran kauyukan da ke makwabtaka da shi. Sabo da manoma ba su yi zama kusa da cibiyar jiyya ba, shi ya sa Ma Yupeng ya kan tuka babur domin zuwa gidajen tsoffi da mata da kuma yara da suka kamu da cututtuka don yi musu jiyya.

Zhang Xiufang da take fama da cutar kirji mai tsanani wata manomiya ta kauyen Dongtang, kullum ta kan nemi Ma Yupeng wajen ganin likita. Lokacin da take tabo magana kan likita Ma, Madam Zhang ta nuna masa godiya sosai. Kuma ta bayyana cewa,

"Wannan cutar da nake fama da ita ta kan barke, muddin na buga masa waya, sai ya zo gidana har da daddare. Likita Ma yana da kirki sosai, kuma kwarewarsa wajen aiki tana da kyau kwarai da gaske. Idan na je gunduma mai nisa domin ganin likita, yawan kudaden da na kan kashe a kan hanya kawai zai kai yuan fiye da goma, shi ya sa ganin likita a kauyenmu yana da araha."

Sabo da mazaunan kauyen Dongtang sun nuna masa sahihanci sosai, shi ya sa Ma Yupeng ba ya son barin kauyen. Muddin Ma Yupeng ya yi tafiya a cikin kauyen, mazaunan wurin su kan gaisa da shi, sabo da haka likita Ma ya kan ji kaunar da suka nuna masa a cikin gaisuwar.(Kande Gao)


1 2 3