Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 16:14:00    
Ma Yupeng, wani likita na kauyen kasar Sin

cri

Ma Zhide, mahaifin Ma Yupeng shi ne tsohon likita ne da ke yin aikin likitanci a kauyen Dongtang har duk rayuwarsa, kwarewarsa wajen aiki tana da matukar kyau, shi ya sa mazaunan kauyen suke nuna masa girmamawa kwarai da gaske. A zaman yau da kullum, Ma Yupeng ya kan koyi yadda ya kamata a yi wa mutane jiyya daga wurin mahaifinsa, ban da wannan kuma idan yana da lokaci, ya kan karanta littattafai a fannin ilmin likitanci. Amma a da Ma Yupeng bai yi aikin likitanci kamar yadda mahaifinsa ke yi ba. Bayan da ya gama karatunsa daga makarantar sakandare, ya koma gida domin aikin gona. A shekara ta 1998, wata dama ta canja makomarsa. Likita Ma ya gaya mana cewa,

"A shekara ta 1998, asusun Amity yana son daukar mutane wajen horar da su don su zama likitocin kauyuka, kuma na shiga wannan kwas din horaswa ta jarrabawa. A wancan lokaci, yanayin cibiyar jiyya ta kauyenmu ba shi da kyau sam. A shekara ta 2004, asusun Amity ya ba mu kyautar kudin Sin wato yuan 5000 wajen gina dakunan cibiyar jiyya, kuma kauyenmu ya samar da kudi fiye da yuan 6000, sabo da haka an kyautata dakunan cibiyar jiyya ta kauyenmu."

Asusun Amity da Ma Yupeng ya ambata shi ne wata kungiyar fararen hula da masu bin addinin Kirista na kasar Sin suka gabatar, kuma mutanen sassa daban daban na zamatakewar al'ummar Sin ke sa hannu a ciki. Nufin asusun shi ne dukufa kan sa kaimi ga bunkasuwar kiwon lafiya da ayyukan koyarwa da kuma abubuwan da ke amfana wa fararen hula.


1 2 3