Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 16:14:00    
Ma Yupeng, wani likita na kauyen kasar Sin

cri

Kasar Sin wata kasa ce da ke da mutane masu yawa, kuma kashi 60 bisa dari daga cikinsu suna da zama a kauyuka. Bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a wasu yankunan kauyukan kasar Sin na baya-baya sakamakon dalilai iri daban daban, kuma yanayin jiyya da kiwon lafiya na wuraren nan ba shi da inganci. Sabo da haka kullum likitocin kauyuka su kan dauki nauyin ayyukan kiwon lafiya na mazaunan wurin bisa wuyansu. Wadannan likitocin kauyuka su kan haye wahalolin da suke sha a fannin yanayin halittu da karancin na'urorin jiyya masu kyau domin samar da ayyukan ba da hidima ga manoma kamar yadda ya kamata, ta haka suna bayar da muhimmiyar gudummowa ga lafiyar manoman da ke da zama a yankuna masu fama da talauci. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wani likitan kauye wanda ake kiransa Ma Yupeng.

Ma Yupeng yana da zama a kauyen Dongtang na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai da ke arewa maso yammacin kasar Sin, inda ake iya samun iska mai karfi sosai amma ruwan sama dan kadan, haka kuma kwararowar hamada tana da tsanani. Likita Ma Yumeng mai shekaru 35 da haihuwa, game da dalilin da ya sa ya zama wani likita na kauye, ya gaya mana cewa,

"Lokacin da shekaruna ya kai 11 da haihuwa, yanayin jiyya da kuma magunguna ba kyau. Wani yaro mai shekaru 7 da haihuwa ya kamu da cutar huhu, bai iya yin komi sai kwanciya a gida har kwanaki uku. Lokacin da iyayensa suka gano cewa, lalle yaron ba ya samun sauki ko kadan, sai suka dauke shi zuwa gidana. Bayan da mahaifina ya yi masa jiyya, ya gano cewa, ba shi da dabarar warkar da shi, shi ya sa aka dauke shi zuwa wani babban asibitin da ke birni, amma wannan yaro ya riga mu gidan gaskiya a kan hanyar zuwa asibiti. Sabo da haka ina ganin cewa, idan akwai wani likita mai kyau a kauyenmu a wancan lokaci, wannan yaro ba zai mutu ba. Shi ya sa na gayawa kaina cewa, ya kamata in koyi ilmin likitanci, da kuma zama wani likita a kauyenmu."


1 2 3