A shekarar 1965, an gano zane-zanen da aka saka su a kan jikin tsauni. Ko da yake har yanzu ba a iya tabbatar da cewa wadannan zane-zane ne da kakanin-kakanin kabilar Wa suka saka ba, amma abubuwan da suke bayyanawa a cikin zane-zane suna da nasaba da zaman rayuwar jama'ar kabilar Wa.
Bisa al'adar kabilar Wa, maza kan sanya falmara irin ta launin baka da wando, amma mata su kan sanya buje tare da dutsen wuya da na hannu da na kafa irin na azurfa.
'Yan kabilar Wa su kan gina gidajensu ne a kan jikin tsauni ko a kan wani tsauni. Bisa al'adar kabilar Wa, wani saurayi yana iya auren mace daya, auta ne ke gadon dukiyoyin iyayensu, amma diyya ba ta da ikon gadon dukiyoyin iyayenta. Matasa suna da 'yancin neman soyayya, amma dole ne iyayensu su tabbatar da aurensu. (Sanusi Chen) 1 2 3
|