Yawancin 'yan kabilar Wa suna zama a lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000 a duk fadin kasar Sin, yawan 'yan kabilar ya kai fiye da dubu 396. Suna amfani da yaren Wa. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, gwamnatin jama'a ta kasar Sin ta tura masana wadanda suka kware kan harsuna domin gudanar da bincike kan yaren Wa. Sannan an kirkiro haruffan yaren Wa bisa haruffan Latin. Kabilar Wa na daya daga cikin tsoffin kabilun da suka dade suna zama a kardin Yunnan.
A cikin litattafan tarihi, an bayyana cewa, muhimman sana'o'in da 'yan kabilar Wa suka taba yi sun hada da sana'ar farauta da kiwon dabobbi tare da kuma tsintar 'ya'yan itatuwa. Wasu sun soma aikin gona irin na matakin farko. Bayan da kasar Sin ta shiga daular Ming da ta Qing, wato yau da shekaru kimanin dari 6 da suka wuce, tattalin arziki da zaman al'ummar kabilar Wa sun samu cigaba sosai.
1 2 3
|