Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 16:12:12    
Takaitaccen bayani game da kabilar Wa

cri

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, an kafa gundumar Menglian ta kabilar Dai da ta Lahu da ta Wa mai cin gashin kanta. Sannan an sake kafa sauran gundumomin kabilar Wa guda 3 a lardin Yunnan. A cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce, tattalin arziki da zaman al'ummar kabilar sun samu ci gaba cikin sauri. An riga an kafa wasu masana'antun zamani a yankunansu, ciki har da tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da masana'antun kera injunan aikin gona da na narke karfe da sarrafa abinci. Bugu da kari kuma, an samu cigaba sosai wajen raya zirga-zirga da sufurin kayayyaki da sha'anin kasuwanci da ilmi da al'adu da kiwon lafiya a yankunan kabilar. Yanzu, kabilar Wa tana da daliban da suka gama karatu daga jami'o'i da asibitoci a kowace gunduma da dakunan likitanci a kauyuka da makarantun firamare da na sakandare a dukkan yankunan kabilar.

Kabilar Wa tana da al'adu iri iri, musamman adabin baka da suke da nasaba da haihuwar dan Adam da kasancewar halittu a duniya da bukukuwan aure da na jana'izza da yadda 'yan kabilar suke aiki yana da launi iri iri.


1 2 3