Malam Li Yizhong, shugaban babbar hukumar kula da hana hadarurruka a wuraren aiki, ya ce, tun daga watan Yuni na shekarar da muke ciki, Sin za ta aiwtar da "ka'idojin ba da rahotannin aukuwar hadarurruka a wuraren aiki da bincikensu", wadanda daga dukan fannoni ne suka tanadi yadda za a ba da rahotanni da gudanar da bincike kan hadarurrukan da suka auku a wuraren aiki da kuma yanke hukunci a kansu.
Malam Li Yizhong ya kuma kara da cewa, sassan da abin ya shafa za su kara karfin gudanar da bincike a kan ayyukan karbar rashawa da suka haddasa hadarurruka. Ya ce,"Bisa tsarin hadin gwiwar sassa da dama, za a yi ta kara karfin binciken ayyukan karbar rashawa da wasa da aiki da musanyar kudi da iko da hadin kan jami'ai da 'yan kasuwa da ke bayan hadarurruka. Sa'an nan za mu kafa wani tsari tare da hukumar tsaron lafiyar jama'a da hukumomin shari'a dangane da yadda za a gudanar da bincike a kan hadarurruka."(Lubabatu) 1 2 3
|