An ce, a yayin da sassan da abin ya shafa ke gudanar da bincike a kan wadannan manyan hadarurruka biyar, an kuma gano mafakar da wasu jami'an da ke cin hanci suka bai wa masu ramukan kwal. A cewar malam Chen Changzhi, mataimakin ministan sa ido na kasar Sin, sassan da abin ya shafa sun gudanar da bincike sosai a kan al'amuran, ya ce,"A yayin da suke gudanar da bincike kan hadarurrukan, sassan sa ido na matakai daban daban sun gudanar da bincike kan masu daukar alhakin hadarurrukan da kuma yanke musu hukunci, a yayin da suka kuma kara karfin binciken neman boye hadarurruka da karbar rashawa da aka yi a bayan hadarurrukan."
Bisa kididdigar da aka bayar da dumi-duminta, an ce, a farkon watanni hudu na shekarar da muke ciki, yawan mutanen da suka mutu sakamakon aukuwar hadarurruka iri iri a wuraren aiki ya ragu da kashi 4.3%. Amma duk da haka, ana ci gaba da kasancewa cikin wani hali mai tsanani a fannin aukuwar hadarurruka a wuraren aiki.
1 2 3
|