Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-10 20:13:37    
Sin ta yanke hukunci kan masu daukar alhakin aukuwar manyan hadarurruka a wuraren aiki

cri
A yau Alhamis, gwamnatin kasar Sin ta bayar da labari dangane da yadda aka yanke hukunci kan manyan hadarurruka biyar, inda aka yanke hukunci a kan masu daukar alhakin aukuwar hadarurrukan da yawansu ya wuce 100 gaba daya, kuma daga cikinsu, an gurfanar da fiye da 50 a gaban kotu. Jami'an sassan sa ido kan al'amuran da abin ya shafa sun ce, Sin za ta kara karfin hukunta ayyukan saba wa ka'idojin aiki da wasa da aiki da karbar rashawa da ke bayan hadarurruka, za su kuma yi kokarin magance aukuwar hadarurruka.

Wadannan manyan hadarurruka biyar sun auku ne yau da shekara guda da ta gabata, inda gaba daya mutane sama da 200 suka riga mu gidan gaskiya, kuma hudu daga cikin hadarurrukan biyar, hadarurruka ne na fashewar ramukan kwal. A gun wani taron manema labaru da aka shirya yau ranar 10 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban babbar hukumar kula da hana hadarurruka a wuraren aiki ta kasar Sin, malam Li Yizhong, a fili ne ya bayyana cewa, bisa binciken da aka yi kan wadannan manyan hadarurruka, an fito fili da wasu matsaloli masu tsanani da ke kasancewa wajen hana aukuwar hadarurruka a wuraren aiki, kuma hadarurrukan sun nuna cewa, wasu wurare da masana'antu ba su tabbatar da manufofi da matakai dangane da hana aukuwar hadarurruka a wuraren aiki yadda ya kamata ba. Ya ce,"Wasu masana'antun da suka sami hadarurruka sun yi biris da dokoki, sun gudanar da harkokinsu ba bisa ka'ida ba. Uku daga cikin hadarurrukan biyar sun auku ne a sabo da haka. Bayan haka, masana'antun da suka sami hadarurruka ba su ba da kariya ga hadarurruka ba yadda ya kamata, shi ya sa akwai babbar yiwuwar samun hadarurruka."


1 2 3