Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-09 17:37:05    
Kasar Sin za ta kara kokari wajen shawo kan cututtuka da ake kamuwa da su a wurin aiki

cri
 

A fannin dokoki, gwamnatin kasar Sin ta bayar da "dokar game da shawo kan cututtuka da ake kamuwa a wuraren aiki" a shekarar 2002, don ba da tabbaci ga shawo kan cututtuka da ake kamuwa a wuraren aiki bisa doka. Nan gaba kuma, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar za ta yi kwaskwarima a kan dokoki da dama kamar "dokar kan fasahar sanya ido kan lafiyar ma'aikata" da sauransu.

A wani bangare daban, hukumomin kiwon lafiya za su kara kokari wajen sanya ido kan harkokin kiwon lafiya da ake yi a wuraren aiki, sa'an nan za su nuna himma ga yin bincike kan cututtuka da ake kamuwa a wuraren gine-gine. Malam Su Zhi, mataimakin shugaban hukumar sanya ido kan aikin kiwon lafiya ta ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya ce, "yayin da ake gudanar da harkokin kiwon lafiya a wuraren aiki a shekarar nan, za a kara kokari wajen sanya ido musamman kan mahakan kwal da masana'antun hada magungunan sha da magungunan kashe kwari da sauransu. An bukaci hukumomin kiwon lafiya na wurare daban daban da su yi bincike kan masana'antu da mutane wadanda suka saba wa "dokar game da shawo kan cututtuka a wuraren aiki" da sauransu, kuma za a yanke musu hukunci bisa dokoki, ta yadda za a kara kiyaye ikon kiwon lafiyar 'yan kwadago." (Halilu)


1 2 3