Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-09 17:37:05    
Kasar Sin za ta kara kokari wajen shawo kan cututtuka da ake kamuwa da su a wurin aiki

cri

A shekarar bara, yawan 'yan kwadago wadanda suka kamu da cututtuka a wuraren aiki ya wuce dubu 11. Malam Su Zhi, mataimakin shugaban hukumar sanya ido kan aikin kiwon lafiya ta ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, wani babban dalilin da ya sa yawan 'yan kwadago wadanda suke kamuwa da cututtuka a wuraren aiki ya yi yawa a yanzu, shi ne domin ma'aikata 'yan ci-rani da suka samu aikin yi a birane da garuruwa sun karu sosai a 'yan shekarun nan da suka wuce, yanzu yawansu ya riga ya wuce miliyan 100. Malam Su Zhi ya ce, "ma'aikata 'yan ci-rani wadanda ke yin aiki a birane da garuruwa su kan canja wuraren aikinsu, sabo da haka da kyar a gano dalilan kamuwarsu da cututtuka a wuraren aikinsu. Yanzu a wasu wurare na kasar, akwai iyalan ma'aikata 'yan ci rani wadanda ke fama da talauci, bayan da ma'aikatan nan suka kamu da cututtuka a wuraren aiki. Sabo da haka cututtuka da ake kamuwa a wuraren aiki wata babbar matsala ce ga tabbatar da zaman jituwar jama'a da aikin kiwon lafiyarsu."

Bisa kimantar da kwararru na cibiyar shawo kan cututtuka ta kasar Sin suka yi, an ce, nan da shekaru masu zuwa, jimlar 'yan kwadago wadanda ke kamuwa da cututtuka a wuraren aiki za ta ci gba da karuwa. A cikin irin wannan hali ne, hukumomin kiwon lafiya na kasar Sin za su dauki matakai daban daban wajen kara shawo kan cututtukan don kiyaye lafiyar 'yan kwadago.


1 2 3